ABNA24 : jaridar Annahar ta kasar Lebanon ta bayyana cewa shugaban kasar ta Faransa ya gana da tokwaransa na kasar Lebanon Michel Aun, inda ya bayyana dalilan zuwansa kasar Lebanon a wannan karon kamar haka.
Da farko ganin inda aka kwana dangane da tallafin da kasar take bukata bayan fashewar da ta faru a tashar jiragen ruwa ta Beirut, wanda ya lakume rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Sannan akwai batun halattan taron cike shekaru 100 cur da kafa kasar ta Lebanon, wanda ya faru a shekara 1920.
Sai kuma don ganin yadda harkokin siyasar kasar suke tafiya a cikin ‘yan kwanakin nan.
Bayan ganawarsa da shugaban kasa, Macron ya gana da fitattun ‘yan siyasar kasar, wadanda suka hada da Sa’adul Hariri, tsohon firai ministan kasar, sannan shugaban jam’iyyar Mustagbal.
342/